labarai
Dalilin Neymar na bayyana ‘yan wasan da sukafi kowanne Iya kwallon kafa

Duk da cewa Neymar dan wasa ne mai hazaka da kansa, tauraron dan kasar Brazil din ya nemi yayi bayanin abin da yayi imanin cewa wanene cikakken dan kwallo. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Ya ambaci halayen Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Zlatan Ibrahimovic, Kylian Mbappe da Sergio Ramos, yana mai cewa haduwar wadannan ‘yan wasan biyar zai zama abin birgewa.
“Cikakken dan wasa? Ina ganin wani wanda yake da surar Cristiano Ronaldo, da yanayin Zlatan, saurin Mbappe da kuma karfin ikon Sergio Ramos shima,” in ji Neymar a wani taron masu daukar nauyin Taron.
“Saidai yace Yana bukatar kafar hagu ta Messi da ta dama, da kuma bugun taren Kante da kirkirar kwallon Verratti, matsayin basirar Lewandowski shi ma.”
Menino zai zama tauraron Amurka ta Kudu nan gaba
Bayan sanya sunansa a Kudancin Amurka tare da Santos, Neymar ya kalli kungiyoyi suna neman fitaccen jarumi na gaba da zai fito daga nahiyar, kuma shi da kansa ya yi imanin cewa mai yiwuwa Gabriel Menino na Palmeiras shi ne mutumin.
Neymar ya kara da cewa “Ina son Gabriel Menino.”
“Yana da kwazo sosai. Na ga wasanni biyu na Libertadores inda ya buga wasa, zai iya haskakawa a Turai. Ni ma ina son Gerson sosai.”