Connect with us

labaran wasanni

Dan Wasan Da Barcalona Zata Bewa Number 10 Messi

Published

on

KU KA KASAN WAYE BARCELONA SUKA BAWA NUNBER 10
TUN TAFIYAR MESSI

Ranar Alhamis Lionel Messi ya bar Barcelona, kungiyar da ya yi
kaka 21 yana buga wa tamaula.
Tuni dan wasan mai shekara 34 ya yi ban kwana da kungiyar
da kuma ‘yan wasa ranar Lahadi da kawo yanzu ya kulla
yarjejeniya da Paris St Germain.
Ranar Lahadi 15 ga watan Agusta Barcelona za ta fara wasan
farko a La Liga kakar 2021-22 ba tare da Messi ba da riga mai
lamba goma.
Kungiyar ta yi wasa ranar Lahadi a karon farko ba tare da dan
kwallon Argentina ba, inda ta doke Juventus da ci 3-0.
A karawar Sergio Busquets ne ya yi kyaftin koda yake ba dan
wasan da ya sa riga mai lamba 10 a ranar.
Messi ya fara sa riga mai lamba 10 a Barcelona cikin shekarar
2008 zuwa 2021, wanda rigar na kasa kawo yanzu.
Ba kasafai ake jingine riga ba a Sifaniya duk kwazon da dan
wasa zai yi a tamuala kamar yadda ake yi a gasar Serie A da
Roma ta jingine rigar Toti.
A Premier League ma Chelsea ta ajiye riga mai lamba 25 da
Gianfranco Zola ya yi amfani da ita, da kuma yadda ake yi a
gasar kwallon kwandon Amurka.
A fannin kwallon kafa riga mai lamba 10 tana da daraja, ana
bai wa fitattun ‘yan wasa da suka kware wajen taka leda da
bajinta.
Duk tawagar kwallon kafa ko kungiya kan auna kwazon dan
wasa kafin ta bashi riga mai lamba 10, kuma duk wanda ya sa
za kaga yana da kwazo ko yaya yake.
Fitattun ‘yan wasa da suka sa riga mai lamba 10 a Barcelona
suka yi suna a duniya sun hada da Romario da Ronaldinho da
Diego Maradona da Rivaldo da kuma Messi.
Jerin wadanda Barcelona ta bai wa riga mai lamba 10 tun da
aka kirkiro sa lamba a rigar tamauala:
1-Angel Cuellar (1995-1996)
2-Giovanni (1996-1997)
3-Jari Litmanen (1999-2000)
4-Rivaldo (2000-2002)
5-Juan Roman Riquelme (2002-2003)
6-Ronaldinho (2003-2008)
7-Lionel Messi (2008-2021)

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *