RONALD KOEMAN
YAZAMA DOLE MU RUFE SHAFIN MESSI A BARCELONA !
Kocin Barcelona KOEMAN yace “dolene saimun rufe littafin Messi idan munaso mu kaiga nasara akakar bana
Koeman yace ” rabuwa da Messi abune Wanda bamu shirya masa ba a wannan lokacin dole kowa yakasan ce acikin yanayi na rashin jin dadi ,amma wannan kalubalen yawuce mun rufe shafinsa,
yanzu abunda yake gabammu shine yadda zamuyi mukaiga nasara a sabuwar kakar da zamu shiga, ashekarar da ta wuce Messi shi kadai yaci mana kwallaye 30 a bana kuma babu shi dole zamu fuskanci kalubale na zura kwallo a raga ,amma saidai munada ‘yan Wasa masu kwarewa sannan inaga wannan shine lokacin da matasan yan Wasa zasu samu dama fiyeda kowani lokaci ,zamu gina kungiyar mu dasu “
Hakanan koeman ya nuna farin cikin sa akan dawowar zakwakuran ‘yan wasan sa guda biyu ANSU FATII da PHILIPPE COUTINHO wayanda aka kammala kakar bara batareda suba .