Carlo Ancelotti yana son Cristiano Ronaldo ya koma Real Madrid
August 17, 2021
Gidan talabijin na Sifen El Chiringuito ya ruwaito wannan sabon Labarin a cikin shirin ta na gidan talabijin din na kasar Sifen.
El Chiringuito ta sanar da sanyin safiyar yau cewa Edu Aguirre, babban abokin Cristiano Ronaldo kuma mai ba da rahoto ga shirin, zai sanar da labarai masu zafi game Cristiano Ronaldo.
A cewarsa, Carlo Ancelotti ya fara tattaunawa da kungiyar don dawo da Cristiano Ronaldo Bernabeu, kuma yana ganin Ronaldo a matsayin wani wanda har yanzu zai iya taimakawa ƙungiyar kuma ganin cewa Ronaldo yana son barin Juventus, yana ƙoƙarin turawa Domin a sa hannu fitaccen dan wasan.
Manajan Madrid yana ba da rahoton wannan labarin, amma ba shi da tabbacin abin da zai faru a zahiri, musamman ganin cewa Florentino Perez ya bayyana a baya cewa Ronaldo ba zai dawo ba, haka kuma duk wani kuɗaɗen da Real Madrid ke da shi za a saka wa Kylian Mbappe ko Erling Haaland.
Zamuyi amfani da wannan don ƙaddamar da tattaunawa kan ko sanya hannu da Ronaldo yanzu yana da ma’ana.
Cristiano Ronaldo Wanda ya Raba gari da Real Madrid bayan kammala gasar cin Kofin Duniya a shekara ta 2018, bayan Komawar sa Juventus a yanzu Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan ya fara nazarin barin Turin.
Wanda hakan yasa Carlo Ancelotti ya Fara sha’awar dawo da fitaccen dan wasan Wanda sukayi aiki tare a Real Madrid a shekara ta 2014 Kuma sun lashe gasar Zakarun Turai tare Akan Atletico Madrid a wannan shekarar.