Connect with us

labaran wasanni

Labaran Safiya: Dembele,  Hazard,  Roberto,  Haaland,  Mertinez,  Abde

Published

on

Labaran Safiya: Dembele,  Hazard,  Roberto,  Haaland,  Mertinez,  Abde

A cewar jaridar marca kungiyar kwallon kafa ta B.Dortmund xata rubanya albashin erling haaland domin ganin bai bar kungiyar ba ixuwa shekara gudu bayan karewar kwantaraginsa
Ko haalanda xai amince da wannan siyasar yanxu dai albashinsa €8m idan ya amince da tsarin xai xama €16m kenan, a halin yanxu barca tana da manyan masu albashi irinsu coutinho €22m, umtiti €15m s.Roberto €9m

A cewar mundo depotivo kungiyar kwallon kafa ta Everton ta nuna sha’awarta matuqa na daukar p.coutinho daga Barcelona, xavi Hernandez mai horas da kungiyar na yanxu yace coutinho baya cikin tsarin dan kungiyar ke kokarin rabuwa dashi a janairu nan

KALAMAN ANCELOTTI AKAN HAZARD DA VINI BAYAN TASHI DAGA WASAN SHEKARAN JIYA

“Sun fahimci abin da kungiyar ke bukata daga gare su ta hanyar tsaro. Sun yi babban aiki Sun yi aiki tuƙuru kuma sun nuna jajircewa sannan kuma sun kawo ƙwazo na gaske a wasan kai hari, musamman tun da wuri. Bambancin, kamar yadda muka fada a baya, yana cikin karewa. Wannan kungiyar ta san yadda za ta ci gaba, za mu iya zura kwallaye saboda muna da fitattun mutane amma muna dan kara kokawa a daya bangaren, amma mun yi aiki mai kyau ya zuwa yanzu”.

“Hazard yana da mahimmanci ga kungiyar, gaskiya ne cewa a matakin mutum daya ya fi taka leda a wannan wasan, a lokacin da ban da tabbas game da shi a zahiri, amma ya yi kyau, na maye gurbinsa a karo na biyu. Ya fafata. , ya gwada abubuwa sama sama. Ya dawo, eh.”Na yarda, Hazard ya dawo.

A cewar ESPN kungiyar kwallon kafa ta Barcelona xatayi maraba ga duk wani tayi akan sergino dest a watan janairu nan, dest dan shekara 21 yana daya daga cikin yan wasan kungiyar farko da barca kesan sayarwa domin farfado da tattalin arxikinta

A cewar as.com kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da AFC ajax sunasan kulla yarjejeniyar tsakanin dest da noussair mazraoui , amma ai xasuyi mana ciko ko

A cewar tot Costa dan wasan Barcelona uosmane dembele ya mikawa barca a rubuce yacewa ya amince ya xai sabunta kwantaraginsa da kungiyar, yanxu haka dan wasan yanada xabi biyu kodai ya sabunta xuwa shekarar 2024 ko har xuwa 2027

A cewar African insider idan abdessamad ezzazouli ya bugawa kasar Morocco wasa a watan mai kamawa baxai bugawa kasar Spain wasa ba shikenan, a baya dai kasar ta spaniya taso dan wasan ya sanya mata riga dan xama dan wasan ta amma da alama hakan baiyuwu ba

A cewar Alfredo Martinez na jaridar sport yace Pablo gavi yana son xama a barca kuma duk mai kaunar daukar yaron a yanxu dole ya biya €1billions domin rabashi da barca, komai na kontaragin gavi xai kammala ne a janairu , albashin dan wasan xai karu saboda yana daga cikin yan wasa mafi karancin albashi a kungiyari inda yake €100,000 duk shekara gsky kudin kam yayi kadan

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *