Connect with us

labaran wasanni

Labaran Wasannin Rana, Anfusata Barcalona, Haaland Yace A Spain Yakeso Yaci Gaba Ga Kwallownsa

Published

on

Labaran Wasannin Rana, Anfusata Barcalona, Haaland Yace A Spain Yakeso Yaci Gaba Ga Kwallownsa

 

A cewar Diario sport kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tayi matukar fusata dan gane da ikirarin wakilin ousmane dembele sannan kungiyar ta kasa fahimtar meyasa dan wasan ya kasa yanke hukunci, dan wasan dan kasar faransa a baya ya fadawa kungiyar cewa xai cigaba da xama amma ya fasa, barca ta dau alkawarin xata masa hukunci irin yadda tayiwa ilax moriba a watannin baya

A cewar Diario as erling haaland ya tambayi masoyansa maye ra’ayinsu dan gane da gobensa a birnin marbela dan wasan dai ya yanke hukunci cewa xai cigaba da wasa a kasar Spain Madrid ko barca ❔

A cewar catalunya radio kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fadawa ousmane dembele cewa kodai ya yarda a saida shi a wannan wata ko kuma a turashi ko kuma bashi hukunci irin na ilax moriba

A cewar Gerrard Romero kocin kungiyar kwallon kafa ta athletico Madrid diago simeone yace bayasan kulla yarjejeniyar morata da Barcelona, kocin na de Madrid bayasan abokan hamayya irin barca su sayi dan wasan tsoro ne ko

A cewar Gerrard Romero xuwan Alvaro morata baxai shafi xuwan erling haaland ma’ana koda morata yaxo haaland xaixo

A cewar gianluca dimazio ta cikin jaridar sky sport kungiyar De Madrid ta bukaci Barcelona ta dauki Alvaro morata amma a matsayin aro tare da xabin sayan dan wasan na dole akan kudi €35m amma fa kungiyar ta Barcelona baxata amince da tsarin ba kuma bata hakura ba

A cewar jaridar el-partidazo cope jiya Joan laporta ya shiga cikin matsi saboda ya sau lafi cewa cigaban dembele xataxo da dadi amma hakan bata samu ba, a cewar laporta dembele ya nunawa barca cewa shi butulu ne bamai godiya bane kungiyar ta Barcelona baxata kara tuntubar sa ba

A cewar Romeo agresti ta cikin jaridar Italian goal tace Alvaro morata ya amince da kontaragin wata sha takwas da Barcelona amma yanxu xuwan dan wasan yana ga juventus dan samun maye gurbinsa

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.