labaran wasanni
Real Madrid za ta san wadda za ta fuskanta a Copa del Rey ranar Juma’a

Ranar Juma’a 7 ga watan Janairu ake sa ran raba jadawalin wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Copa del Rey ta bana.
Jadawalin da za a gudanar a hukumar kwallon kafar Sifaniya zai fayyace kungiyar da Real Madrid za ta fuskanta, bayan da ta yi waje da Alcoyana.
Watakila a hada Real da wata karamar kungiyar a zagayen gaba, wadda ta taka rawar gani a fafatawar kungiyoyi 32.
Wasu kungiyoyin da suka kai bantensu sun hada da mai rike da kofin, Barcelona da Espanyol da Real Sociedad da Mallorca da Valencia da Atletico Baleares da Betis da Rayo Vallecano da sauransu.
Za a buga wasannin kungiyoyi 16 da suka rage sau daya tsakanin 19 ko kuma 20 ga watan Janairun 2022.
Idan aka hada Real da karamar kungiya, ita ce za ta kai ziyara kenan, idan kuma aka hada ta da sa’arta, watakila Real ta zama mai masukin baki.
Idan aka kammala wadan nan wasannin za a fada karawar daf da na kusa da na karshe daga 2 ga watan Fabrairu, sannan fafatawar daf da karshe da za a yi gida da waje ranar 9 ga watan Fabrairu da kuma 2 ga watan Maris.
Za kuma a bugan wasan karshe ranar 23 ga watan Afirilu a filin wasa da ake kira Estadio La Ca rtuja.