labaran wasanni
TAKAITATTUN LABARAN REAL MADRID NA YAMMACIN YAU

TAKAITATTUN LABARAN REAL MADRID NA YAMMACIN YAU
🚨Duka yan wasan Real Madrid wadanda basa nan Courtois, Benzema, Modrić, Mendy da Vinicius sun dawo atisaye.
Bale da Carvajal har yanzu suna bukatar karin lokaci domin atisaye da tawagar. Jovic har yanzu bai warke daga corona ba Mariano kuma ya samu rauni.
🚨 Official:
HERNANDEZ HERNANDEZ shine zai jagoranci wasan Real Madrid da Valencia a Santiago Bernabeu ranar Asabar.
🚨Dalilin da yasa ba a kira yan wasan karamar kungiyar Madrid da yawa ba:
Ancelotti ya yanke shawarar daukar gasar mai muhimmanci, kuma na biyu.
[AS]
🚨 Mafarkin Dusan Vlahovic shine ya taka leda a La Liga ko kuma ya cigaba da zama a Italy, idan haka bai yiwu ba, zai maida hankali wajen komawa Premier League.
[AS]
🚨 Real Madrid bazata siya Haaland ba. Kungiyar tafi maida hankali ne kawai akan Mbappé kuma bata kokarin siyan Haaland a shekarar nan. Zai zama zabin kungiyar ne kawai idan ya cigaba da zama a Dortmund har zuwa 2023, idan kwantiragin Benzema ya kare.
[Tomas González M]
🚨 Mahaifin Erling Haaland, Alf-Inge Haaland, yana son dan shi ya koma Real Madrid.
[Josep Pedrerol]
🚨 Real Madrid bata damu da surutan da Joan Laporta yake yi ba game da Erling Haaland. Haaland ya fifita Real Madrid akan kowace kungiya kuma kungiyar ma ta sani.
[AS]
🚨 Laporta yana iya bakin kokarin shi don ganin ya siya Haaland. Kuma FC Barcelona basa son ganin Madrid ta hada Mbappé, Vinicius da Haaland a matsayin yan wasan gaba.
[Marca]
🚨 Marcelo, Isco da Bale zasuyi bankwana da Real Madrid a karshen wannan kakar. Luka Modrić yana son yayi ritaya a Madrid.
[SQuirante]
HalaMadrid 🤍