labaran wasanni
An kai Franck Ribery asibiti bayan da ya yi hatsarin mota Ya faru ne a safiyar Lahadi

Franck Ribery ya samu ‘dan rauni a kansa bayan da ya yi hatsarin mota, kuma zai yi jinyar wasu ‘yan kwanaki a matsayin riga-kafi.
Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata, yayin da motar ta yi karo da na’urar lura da ababen hawa a garin Laura di Capaccio Paestum da ke lardin Salerno na kasar Italiya.
A cewar Il Corriere dello Sport, Ribery, wanda ba ya tuka motar, an garzaya da shi asibiti kafin a ba shi haske ya koma gida.
A halin yanzu, Salernitana ita ce ta karshe a gasar Seria A da maki 15 kacal bayan wasanni 25 da aka buga. Ribery ya koma Salernitana a bazarar da ta wuce bayan Fiorentina ta sake shi.